Friday, 20 October 2017

Tayi Aure da cikin shege


Tayi aure da cikin shege

Tambaya:
Assalamu alaikum. Malam wata ta yi cikin shege da wani mutum, sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta. Yanzu sun yi auren, yaya hukuncin auren shari'a ya ke?

Amsa:
Wa alaykum assalamu, zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan kasa. Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka.
Kuma an kwadaitar da mu yin sa. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.

Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi`i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba.

Kuma suka kara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ya ce: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to ka da ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa." Abu- dawud : 1847. Don neman karin bayani duba : AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79.

A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin a yi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma zaba kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, sai dai ya wajaba şu nisanci saduwa, kafin ta haihu saboda hadisin da ya gabata. Allah ne mafi sani.

2. HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A SAKETA
TAMBAYA
Assalamu alaikum Malam. Mace ce aka aurar tana 'yar-shekara 14 ga wanda ba ta so, to sai mijin yayi tafiya har tsawon wata hudu (4) To sai matar tasa aka rubuta mata saki ta ce ya sake ta, bayan ya dawo ya ce bai sake ta ba, amma ba'a yarda ba.
Da ta kare idda tayi aure da wani har suka haihu, daga baya kuma suka rabu, kuma yanzu ta ga musifu suna ta samunta, sai take tunanin ko wancan abin ne da ta yi. Tana neman fatawa, ina hukuncinta, da yaran da ta haifa da miji na biyu?

AMSA:
Wa alaikum assalam
Malam amsar wannan tambaya yana da mutukar wahala, sai dai na nemi taimakon wasu daga cikin malamaina, ga abin da na samo :
1. Abin da ta yi mummuna ne a shari'ar Musulunci saboda ta yi aure cikin aure.
2. Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.
3. Yaran da su ka haifa da mijnta na biyu, 'ya'yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya.
4. Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce sai dai in ya sake ta.
5. Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, sai dai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya.
6.Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubin da ta aikata.
7. Zai yi kyau su je wajan alkali wanda ya san shari'ar Musulunci, domin ya yi musu hukunci.

Allah ne mafi sani.

Nigeria ta kusa rugu rugu: inji kungiyar kiristoti yan majalisaA ranar Larabar da ta gabata ne kungiyar kirista ta 'yan Majalisa ta yi hasashen cewa, kasar Najeriya kadan take jira ta yi uwar watsi. don kuwa za ta yi rugu-rugu.

'Yan majalisar sun kuma yi korafin biyan bukatun al'ummar kasa ya yanke wanda ita ce babbar manufar gwamnati domin 'yan Najeriya da dama su na kangin wahalhalu na rayuwa don kuwa ko bukatun su na yau da kullum ba sa iya biya kawunan su.

Hausa7.tk ta ruwaito daga 'yan majalisar cewa, wannan kalubale da al'ummar Najeriya ke fuskanta ta sanya su sun cire tsammani a cikin shugabancin kasar., wanda kawai yanzu Najeriya ikon Rabbani suka zubawa idanu wajen agajin kasar daga fadawa cikin wani hali da ba zai musaltu ba.

'Yan majalisar na gwamnatin tarayya karkashin kungiyar kirista ta 'yan majalisu sun yanke shawarar cewa, za'a gudanar da addu'o'i a ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba ta mako mai gabatowa domin ceto kasar nan ta hanyar rokon dauki daga Ubangiji.

Yayin ganawa da manema labarai a ranar da gabata akan tsare-tsaren gudanar da addu'o'in, shugaba mai gudanar da addu'o'in Sanata Barnabas Gemade, na jam'iyyar APC mai wakilcin Arewacin jihar Benue ya bayyana cewa, wannan tsarin na gudanar da addu'o'i ya samo tushe ne shekaru 7 da suka gabata da sanadin kwaikwayon kasar Amurka wanda tsohon shugaban kasa Dwight Eisenhower ya fara aiwatar wa a shekarar 1953.

Sanata Barnabas ya bayyana cewa, tun shekaru bakwai da suka gabata, najeriya take fuskanatr kalubale na fitintinu kama daga zamantakewa da kuma tattalin arzikin kasa, wanda da ba don ire-ire wannan kalubale ba wani labarin daban za a ji na bankayi a kasar nan.

Ya kara da cewa, shugaban kasa Muhammadu shine zai zamto babban bako na musamman a wajen gudanar da addu'o'in, yayin da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo zai gabatar da jawabai na musamman.

Thursday, 19 October 2017

Wani Dan Banga yakashe Ango saura kwanaki kadan daurin aurensaWani matashi mai suna Ndubuisi Oye wanda yake tsakiyar shire-shiren auren sa ya gamu da ajalin sa a hannun wani dan banga a garin Ogbunike dake a karamar hukumar Oyi ta jihar Anambra dake a kudu maso gabashin kasar na kwanaki shidda kacal kafin auren sa.


Majiyar mu dai har ila yau ta ruwaito cewa haka zalika ma dai dukiya ta dubban nairori ta salwanta sanadiyyar kisan da aka yi wa matashin a ranar Litinin din da ta gabata da dan bangar mai suna Levi Elobis yayi masa.


Hausa7.tk ta samu dai cewa waddan matashin zai aura Mis Oluma Agbugba ta shaidawa manema labarai cewa: "Al'amarin ya faru ne yayin da muke dawowa daga wani taron kwamitin abokan mu inda ake ta shirye-shiryen yadda za'a yi bukin auren na mu ranar Lahadin nan mai zuwa."


Ta ci gaba da cewa: "Muna kan hanyar mu ta dawowa ne sai kawai yan bangar suka tare mu suka kuma kwantar da mu a kasa kafin daga bisani daya daga cikin su ya harbe mun ango har lahira."
Kwamishinan 'yan sandan jihar Garba Umar ya tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma bayyana cewa sun kama wanda ake zargin kuma suna ci gaba da binciken sa.

Rikicin Atiku da Gwamnati: Yan majalisar tarayya sun goyi bayan Atiku
A jiya ne dai yan majalisar wakillan Najeriya suka tsoma bakin su a cikin takaddamar da a halin yanzu ke ci gaba da wakana tsakanin hukumar dake kula da tashoshin jiragen ruwa ta gwamnatin tarayya watau Nigeria Ports Authority (NPA) karkashin jagorancin Uwargida Hadiza Bala Usman a turance da kuma kamfanin Intels mallakin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar.
Tsomabakin na majalisar dai ya biyo bayan wani kudiri mai muhimmanci da dan majalisa Diri Douye daga jihar Bayelsa ya kawo yana mai bukatar majalisar ta kafa wani dan kwarya-kwaryar kwamitin bincike da zai gano gaskiyar lamarin da ya jawo dakatar da kwantaragin da kamfanin ke yi da hukumar.

Hausa.tk ta samu dai cewa jim kadan bayan da majalisar ta yanke shawarar kafa kwamitin tare kuma da basu kwanaki bakwai su gabatar da rahoton su sai suka umurci hukumar ta NPA da ta janye dakatarwar da tayi wa kamfanin har sai kwamitin nata ya kammala binciken sa.

Kafin dai majalisar ta amince da kafa kwamitin yan majalisar sun tafka zazzafar muhawara dangane da batun inda wasu ke ganin hukumar tayi dai-dai da ta dakatar da kamafanin wasu kuma na cewa bata yi dai-dai ba.

Sana'ar yankan kai tamin komai


Sana’ar Yankan Kai Ta Yi Min Komai, Na Ci, Kuma Na Sha – In Ji Dattijon Biri.

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta kama wani fitaccen dattijon biri mai sana’ar saye da sayar da naman mutum tare da kawunan mutane.


Kwamishinan 'yan sandan jihar Ogun, Ahmed Iliyasu ya bayyana wa manema labaru cewa gungun matsafan da ke karkashin jagorancin wani tsoho mai shekaru 67, Lateef Aremu tare da dan amshinsa, Kola Sadipo sun shahara ne wajen sayen sassan jikin mutane domin tsafi da su.

A wasu lokuttan ma su kan bi makabartu su hako sababbin gawawwakin da aka binne, kamar yadda Aremu ya shaida ma majiyar 
mu, inda ya ce sun samu kudi da harkar sosai.
“Ni manomi ne, kuma Boka ne, wata rana ne za mu yi gini, da muka haka ramin fandisho, sai muka ci karo da kasusuwan mutum, daga nan ne fa na shiga harkar tsafi da kasusuwan, kuma na samu kudi, don tun daga 1980 da na fara zuwa yanzu, na gina gidaje 2 da kuma motoci 15.” In ji Aremu.

Shi kuwa, Sadipo, mataimakin Aremu ya musanta zargin da ake musu, inda ya ce “Ni manomi ne, kuma na san Baba Aremu boka ne, kuma nima na koyi aikin bokanci. Wata rana wani mutum ya zo akan a yi masa tsafin kudi, sai na tura shi wajen Baba Aremu, inda na samu N75,000 duk da cewa tsafin bai yiwu ba. Amma gaskiya ni bani da masaniya akan wasu kasusuwan kai.”

Tuesday, 17 October 2017

Rigar Da Inkasa zaka bace: ba tsafi sai kimiya da fasaha.
Kamar yadda kowa ya sani cewa akwai mutane wadanda suke jingina bango, wato subi ta jikin gini su bace, to yanzu an fara bacewa ta hanya mai kyau ba irin hanyan amfani da sihiri ko kafirci ba.Kamar yadda kowa ya sani cewa sihiri ko tsafi kafirci ne. A zamanin da da yanzu akan sami mutane masu bacewa su shiga gida koda kuwa gidan a kulle ne su kuma iya shiga daki koda kuwan dakin a kulle yake saboda suna bacewa daga zaran sun jingina jikinsu a bango. Amma wannan hanyan kafirci ne, saboda tsafi ne.

Amma yanzu an sami hanyan da ake bacewa ba tare da an yi amfani da sihiri da tsafi ba. Wannan kuwa ba wata hanya bace ba illa hanyace ta amfani da infrared rays. Infrared rays ilimin kimiyya ne da fasaha wanda yake samar da signal wanda idon dan adam baya iya ganin wannan signal din. A jikin remote na TV akwai wani koyi wanda yake samar da signal tsakanin remote din da TV. Wannan dan koyi ya amfani ne da infrared rays.

Infrared rays kan tura sako ko kuma umarni ne ta yadda idanuwan dan adam baya iya gani. Shi yasa idan ka danna remote control zaka ga ya umarci TV da ya aikata wani abu ba tare da wani yaje ya taba TV din ba. Misali idan ka yi pressing din volume key a jikin TV remote sai ka ga TV din ya kara ko rage volume din sa.

To da wannan fasahar remote din dake amfani da infrared rays signal yanzu aka hada wata riga wacce idan mutum ya saka kuma ya kunna to rigar zata bi hanyar rays (daman idanuwar dan adam basa iya ganin infrared rays) ta bace.

Ko meyasa wannan rigar take bacewa? Dalili shine a duk lokacin da ka saka rigar ka kunnata to zata yi generating din signal ne, ita kuwa signal bata bin kowace hanya sai hanyan infrared rays, shi kuma infrared rays idanuwa dan adam basa ganinsa, shiyasa idan rigar ta samar da signal to hatta kai da ka saka rigar zata bi da kai ta hanyar da kai ma idanuwa basa iya ganinka. Harma zaka iyabin jikin bango ko ka shiga daki koda kuwa dakin a kulle ba tare da wani yaganka ba.

Wallahi wannan kimiyyar babu shakka ba kafirci bane, domin Allah dakansa ya rantse da hanyar infrared kamar yadda malamai suka fassara aya ta farko a cikin suratul-buruuj. Ina fatan mai karatu ya gane sirrin yadda al'amarin yake.

Macen dake da wahalar samuwa a wannan zamaniMacen Da Ke Da Wuyar Samu A Yau .

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Ya kamata mu sani cewa mace daya ce a duniya take da wuyar samu, amma idan ka samu irinta, kada ka kuskura ka rabu da ita.

Ya halatta ka auri mace fiye da daya, amma Ka sani, mace daya ce kawai, take yin tasiri a rayuwa, wacce ranka kullum zai kasance a kanta.

Babbar tambaya a nan ita ce, wacece wannan dayar? Ita ce wadda duk da namiji yake muradin samu a rayuwarsa, ita ce wacce ke koyi da rayuwar shugabar matan duniya kuma diya ga Rasulallahi (SAW), wato Nana Fatima (Allah Ya kara mata yarda).

Haka kuma ita ce wacce kowace mace take fata ta zama. Ga siffofinta guda goma, Kamar haka:

1. Matar da ta yarda ita mace ce, don haka ta tanadi duk abin da ake bukata a wajen mace.

2. Mace mai hikima da azanci, wacce ta karanci mijinta da kyau, kuma take kauce wa duk abin da zai haddasa matsala a tsakaninsu.

3. Mace mai taushin hali da nutsuwa, wacce miji yake jin natsuwa idan yana tare da ita.

4. Mace da kudi bai dame ta ba, ita mijinta kawai take so, ko da akwai ko babu.

5. Mace mai hakuri da juriya, babu gunaguni, babu mita, da kai kara ga iyaye ko kawaye.

6. Macen da ta dauki kanta likita, mijinta mara lafiya, domin ya sami kulawa, ta
musamman da riritawa.

7. Mace mai saurin daukar ishara, tana gane shiru da magana, da motsi da yanayin shigowa da fita, samu da rashi da kuma yanayin da ake ciki a duniya ko a gari.

8. Mace mai sakakkiyar zuciya, mara kulli da ramuwa.

9. Mace mai karawa miji kuzari da karfin hali, a kan kyawawan manufofinsa.

10. Mace mai rikon amanar aure, da soyayya ga mijinta kawai.

Tarihin Ministotin Mulkin buhari


Tarihin Ministotin mulkin buhari.

1. Babatunde Fashola, Ya yi gwamnan jihar Lagos daga shekarar 2007 zuwa 2015. Dan shekaru 52, Fashola lauya ne kuma ya taba rike mukamin shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin jihar Lagos a zamanin mulkin, Bola Ahmed Tinubu.

2. Cif Audu Ogbeh, daga jihar Benue. Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne kuma ya taba rike mukamin ministan sadarwa a zamanin mulkin shugaba Shehu Shagari. Ogbeh mai shekaru 68, ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya.

3. Hadi Sirika, tsohon Sanata ne daga jihar Katsina. Kuma ya taba zaman dan majalisar wakilai daga 2003 zuwa 2007. Sirika tsohon matukin jirgin sama ne.

4. Abubakar Malami SAN, Babban lauye ne kuma ya taba rike mukamin shugaban kula da bangare shari'a na tsohuwar jam'iyyar CPC ta shugaba Buhari.

5. Kayode Fayemi, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya shafe shekaru hudu a kan kujera kafin ya sha kashi a lokacin yana neman wa'adin mulki na biyu. Inda Ayo Fayose na jam'iyyar PDP ya samu galaba a kansa.

6. Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan jihar Rivers daga 2007 zuwa 2015. Dan jam'iyyar PDP ne kafin ya sauya sheka ya koma APC. Shi ne ya jagoranci yakin neman zaben shugaba Buhari.

7. Udoma Udoh Udoma, tsohon Sanata ne daga jihar Akwa Ibom daga shekarar 1999 zuwa 2007 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP. Ya yi takarar gwamna amma bai samu nasara ba.

8. Ahmed Musa Ibeto, tsohon mataimakin gwamnan jihar Niger daga shekarar 2007 zuwa 2015. Ya raba gari da tsohon mai gidansa, Muazu Babangida Aliyu, shi ne yasa ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC.

9.Kemi Adeosun, tsohuwar kwamishiniyar kudi ce a jihar Ogun. Ta karanta fannin tsimi da tanadi a Ingila kuma ta shafe fiye da shekaru 23 tana aiki a fannin tattalin arziki.

10. Suleiman Adamu - dan jihar Jigawa ne. Kuma Injiniya ne wanda ya shafe shekaru yana aiki. Dan Sarkin Kazaure ne kuma ya yi karatu a jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya da kuma jami'ar Reading ta Ingila. Adamu ya yi aiki da Afri Projects kamfanin da ke lura da kwangilolin PTF.

11. Emmanuel Kachikwu, shi ne shugaban kamfanin mai na Nigeria NNPC. Dan jihar Delta ne kuma tsohon ma'aikacin Exxon Mobil ne wanda ya karanta fannin shari'a a jam'iyyar Nsukka.

12. Janar Abdulrahman Dambazau, tsohon babban hafsan sojin kasa a Nigeria. Dambazau dan jihar Kano ne kuma yana da digirin-digirgir.

13. Aisha Alhassan, ta yi takarar gwamna a jihar Taraba amma ta sha kaye a hannun Darius Ishaku na jam'iyyar PDP. 'Yar majalisar dattijai ce daga 2011 zuwa 2015 an zabi Aisha Alhassan a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kafin ta koma APC.

14. Lai Mohammed, tsohon kakakin jam'iyyar APC ne daga jihar Kwara. Kuma tsohon ma'aikacin hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nigeria ne watau FAAN.

15. Chris Ngige, tsohon gwamnan jihar Anambra ne kafin ya sha kaye a kokarin tazarce inda Peter Obi na jam'iyyar APGA ya samu galaba a kansa. Ngige ya yi Sanata daga 2011 zuwa 2015.

16. Amina Ibrahim, tsohuwar mai bai wa shugaban Njeriya shawara a kan harkokin muradun karni a zamanin mulkin Cif Obasanjo da kuma marigayi Umaru Yaradua. Ta yi aiki tare a ofishin babban sakatare na majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon.

17. Ogbonnaya Onu, shi ne gwamna na farko a jihar Abia daga 1992 zuwa 1993. Ya taba rike mukamin shugaban jam'iyyar ANPP na kasa kafin kafa jam'iyyar APC. Onu ya yi karatu a jami'ar Lagos da kuma ta California a Amurka.

18. Solomon Dalong, dan jam'iyyar APC ne daga jihar Filato. Ya yi takarar gwamna amma Simon Lalong ya doke shi a zaben fitar da gwani.

19. Adebayo Shittu, dan jihar Oyo ne. Kuma ya yi takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar CPC a shekara ta 2011 inda Abiola Ajimobi na jam'iyyar ACN ya samu galaba a kansa. Shittu kwararren lauye ne.

20. Osagie Ehanire, dan jihar Edo ne. Shi ne shugaban gidauniyar TY Danjuma kuma kwararren likita ne wanda ya shafe shekaru yana aiki a babban asibiti na gwamnatin tarayya da ke Benin.


Ina mamakin yadda ma'aikata ke rayuwa ba albashi: abunda buhari ya tuhumi gwamnoni yauShugaban kasa Buhari na ganar sirri da gwamnoni Nigeria.

Shugaban kasar ya tattauna dasu akan yadda suke gudanar da milkinsu a jahohinahohin su. sannan yake tambayarsu yadda suke gudanar da albashi a jahohinsu.

Buhari Yace:


Ina Mamakin Yadda Ma'aikata Ke Rayuwa Babu Albashi, Kamar Yadda Shugaba Buhari Ya Fadawa Gwamnoni.

"Ina mamakin ta yaya mutum zai kwanta ya yi barci ba tare da ya biya ma'aikata albashi ba? Ta yaya ma'aikata suke ciyar da iyalan su, su biya kudin hayar gidan su da kudin makarantar yara?" A cewar Buhari.

A nasa jawabin shugaban gwamnoni Abdulaziz Yari cewa yayi, sun gaji basussuka ne da kuma ayyukan da ba a kammala ba. Amma kudaden daukin gaggawa da na Paris Kulob da suka karba sun yi amfani da su ta hanyar da ya dace.

Wani Da yakamu da cutar kyandar biri yakashe kansaDaya daga cikin mutae 21 da suka kamu da cutar kyandar biri a jahar Bayelsa ya kashe kan shi a jiya Litinin a gurin da aka kebe su da ke asibitin koyarwa na Niger Delta, a Yenagoa babban birnin jahar.

Yayin da ya ke sanar wa manema labarai, kwamishinan lafiya na jahar Ebitimitula Etebu ya nuna takaicin sa game da faruwar wannan abu duba da yadda gwamnati jahar ta ke iya kokarin ta na kula da wadanda suka kamu da cutar da dakile yaduwar ta.

Ya ce bayanan kiwon lafiya na mamacin ba su nuna cewa ya na da tabin hankali ko tsananin damuwa ba, sai da ya ce za su kara bincike domin su samu karin haske game da musabbain faruwar lamarin.

Mista Etebu ya ce tuni suka sanar da ‘yan sanda da iyalin mamacin. Ya kuma kara jaddadawa cewa gwamatin jahar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kawo karshen yaduwar cutar cikin kankanin lokaci.